<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>Ya Hasken Ƙauna, Ƙaunar Allahna LW217</title>
<lyrics>[V1]
 1) Ya Hasken ƙauna, ƙaunar Allahna,
 Ka haskaka.
 Rana ta faɗi, dubu ma ya yi,
 Ka haskaka.
 Wahalar raina duk ta danne ni,
 Amma, ya Haskena, ka bishe ni.

[V2]
 2) Na daɗe fa, kai na ke ta nema,
 Ka haskaka.
 Kai shugaba ne, Hasken gaske kuwa,
 Ka haskaka.
 Duk zunubaina suna ƙaruwa
 Amma, Mai Ceto, zo, ka haskaka.

[V3]
 3) Kai shugabana ne har abada,
 Ka haskaka.
 Ba wanda na ke so dai kamarka,
 Ka haskaka.
 Sha'anin duniya ba su ja ni ba,
 Na ci nasara domin giciyenka,

[V4]
 4) Har ran da za ka zo ka karƃe ni,
 Ka haskaka.
 Ko duhu ne, ko ciwo na ke ji,
 Ka haskaka.
 Zan kwana lafiya a hannunka
 Har ma in farka cikin ƙaunarka.</lyrics>
<hymn_number>217</hymn_number>
</song>